On Air Now

Off Air

Midnight - 5:00am

Kotu Ta Bada Umarnin Kayyade Farashin Kayan Masarufi

KAYAN ABINCI

A yayin da ake tsaka da zanga-zangar halin tsi-tsi a kasar nan, A yanzu haka wata Babbar kotun tarayya dake zamanta a Legas ta amince da wata bukata, wadda ke neman ‘kayyade farashin kayayyaki a kasar nan, nan da kwanaki bakwai masu zuwa.

Mai shari’a Lewis Allagoa ne  ya bayar da wannan umarni biyo bayan karar da lauyan nan mai rajin kare hakkin Dan adam, Femi Falana SAN ya shigar  gaban kotun.

Falana ya maka ministan shari’a  na kasa da Hukumar  kayyade farashin kayayyaki gaban kotun, Inda yake neman ayi amfani da karfin dokar  daidaita  farashin kayayyaki ta kasa, domin kayadde  farashin kayayyaki a Najeriya.

Bayan zaman kotun na jiya Laraba,  Ta baiyana cewar kasancewar  babu wanda  ya soki da’awar mai ‘kara, a saboda haka  ta amince da bukatar  daidaita farashin kayayyaki a kasa.

Kotun ta umarci wadanda ake kara, dasu gaggauta ‘kayyade farashin kayayyaki  kamar su  Madara da Fulawa da Gishiri da Sukari da Keke sai Ashana da Babur da Motoci da  farashin Man fetir da Kananzir da sauransu.