On Air Now

ZANGON RANA

10:00am - 3:00pm

Kotu Ta Dakatar Da Gwamnatin Kano Daga Binciken Batan Kudaden Kananan Hukumomi Naira Billiyan 100

Wata babbar kotun tarayya da ke zamanta a Kano ta dakatar da hukumar karbar korafe-korafen jama’a da yaki da cin hanci da rashawa ta jihar Kano daga binciken zargin batan Naira biliyan 100 daga asusun kananan hukumomin jihar.

Kotun karkashin jagorancin mai shari’a S.A. Amobeda, a ranar Talata ta kuma dakatar da hukumar yaki da cin hanci da rashawa da jami’anta daga gayyatowa ko bincike ko kamawa da tsoratar da shugabannin kananan hukumomi har sai an yanke hukunci kan karar da aka shigar.

Kotun ta bada umarnin dakatarwa ne a kan takardar da Lauyan masu kara  Morgan C. Omereonye ya shigar.

A ranar Talata ne dai hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta ce ta fara bincike kan zargin karkatar da kudaden da gwamnatin da ta shude ta Abdullahi Ganduje ta yi.

Hukumar ta yi zargin cewa ta bi diddigin yadda aka karkatar da wasu kudaden cikin shekaru hudu.

Masu shigar da karar gaban kotun sun hadar da shugabannin kananan hukumomin Dawakin Tofa da Ungogo da Dambatta da  Kunchi da Rimin Gado da  Karaye da Bichi da Tsanyawa da Gwarzo da Tarauni da  Dala, da Tudun Wada da  karamar hukumar birni da kumaShanono.

Wadanda ake kara sun hada da hukumar korafe-korafe da yaki da cin hanci da rashawa ta jihar Kano da shugabanta Muhuyi Rimin-Gado.

Mai shari’a Amobeda ya dage ci gaba da sauraron karar har zuwa ranar 20 ga watan Yuli da muke ciki.