On Air Now

Off Air

Midnight - 5:00am

Kotu Ta Dakatar Da Hukumar DSS Daga Kama Gwamnan Babban Bankin Najeriya CBN

Wata babbar kotun tarayya da ke zamanta a Abuja ta ki amincewa da bukatar da hukumar tsaro ta farin kaya DSS ta gabatar ta neman kama gwamnan babban bankin kasa CBN, Godwin Emefiele tare da tsare shi.

Kotu ta dakatar da hukumar DSS daga kama gwamnan babban bankin kasa  CBNMai shari’a JT Tsoho, yayin da ya ke kin amincewa da bukatar, yace hukumar DSS ba ta bayar da wata kwakkwarar hujja da zata tabbatar da ikirarin da ta yi na cewa Emefiele na da hannu wajen bayar da kudaden daukara nauyin  ta’addanci da kuma laifukan tattalin arziki.

Sai dai alkalin ya ce kamata ya yi a dauki shugaban na CBN idan har akwai wata shaida da ke tabbatar da zargin a cikin takardar.

Kotun ta nunar  da cewa kamata ya yi  irin wannan bukata ta samu amincewar shugaban kasa saboda babban illar da ke tattare da bukatar akan  tattalin arzikin Najeriya idan aka kama gwamnan na CBN.