On Air Now

ZANGON DARE

8:00pm - Midnight

Kotu Ta Daure Wani Sanata Shekara 7 A Gidan Gyaran Hali

Wata reshen Kotun Daukaka Kara dake zamanta a birnin Ikko, Ta yankewa Sanata Peter Nwaoboshi Mai wakiltar Delta ta Arewa,a majalisar dattawa, hukuncin daurin shekara 7 a gidan gyaran hali.

Kazalika Kotun ta umarci a rufe wasu kanfanoninsa biyu, wanda suka hada da Golden Touch Construction Project Ltd da Suiming Electrical ltd , kamar yadda  yake bisa  sashi na 22 na dokara  yaki da aikata almundahanar kudi ta shekarar  2021.

Yanke hukuncin ya biyo bayan karar da Hukumar EFCC  ta daukaka a  gaban kotun, inda take kalubalantar  hukuncin da mai shari’a chukwujekwu Aneke na Babbar kotun taraiyya ya yanke a ranar 18 ga watan yuni, inda ya wanke tare da sallamar wanda ake kara kan wasu tuhume-tuhume biyu da suka danganci aikaya almundahanar kudi.