On Air Now

ZANGON SAFIYAR LAHADI

5:00am - Noon

Kotu Ta Hana Babban Bankin Kasa Tsawaita Lokacin Yin Amfani Da Tsaffin Kudi

SABBIN KUDI

Shin kana daya daga cikin mutanen dake tsammanin babban bankin kasa CBN zai kara lokacin yin amfani da tsaffin kudi, yan naira 200 da 500 da kuma Dubu 1, bayan karewar wa’adin ranar 10 ga watan da muke ciki da bankin ya bayar? To idan har haka ne ya kamata ka sake yin karatun ta nutsu domin yin abunda ya kamata kafin kurewar lokaci.

Hakan  ya  biyo bayan  yadda  wasu  jam’iyyun  siyasa  guda  hudu, suka samu  wani umarni  na wucin gadi  daga  wata  babbar  kotun taraiyya wadda  ta  hana Babban bankin kasar  kara  lokaci  kan yin amfani da tsaffin kudin,  daga  bayan  ranar  10  ga watan da muke ciki na Fabarairu.

Jam’iyyun sun hada da A A Sai  A P P  Da A P M  Da kuma jam’iyyar  NSM.

Kotun ta bada umarnin hana babban bankin kasa da  shugaban kasa Muhammadu Buhari da sauran  bankunan kasuwanci  27 daga   cigaba da  yin amfani da tsaffin kudin, daga  bayan  ranar  10  ga watan da muke ciki.