On Air Now

ZANGON RANA

10:00am - 3:00pm

Kotu Ta Hana DSS Cigaba Da Tsare Godwin Emefiele

DSS

Wata bababr kotun taraiyya dake zamanta a Abuja tayi watsi da bukatar Hukumar tsaro ta farin kaya DSS wadda ke neman a bata damar ci gaba da tsare dakataccen gwamnan babban bankin kasa, Godwin Emefiele har nan da makwanni biyu masu zuwa

Mai shari’a Hamza Mu’azu ya baiyana bukatar a matsayin cin fuska ga hurumin da kotun ke da shi.

Hukumar  ta DSS ta karkashin lauyoyin sun shigar da  karar ne gaban kotu saboda  wasu hujjoji da suka  gabatar.

Sabuwar bukatar da hukumar tsaro ta farin kayan ta shigar ta biyo  sake  damke  Godwin Emefiele da ta  yi a harabar babbar kotun taraiyya  dake  Legas, wadda  ta  bada umarnin cigaba da tsare shi a  gidan gyaran hali, zuwa  lokacin da zai cika  sharuddan bada  shi beli.