On Air Now

ZANGON MARAICE

3:00pm - 8:00pm

Kotu Ta Hana Ganduje Ciwo Bashin Bilyan 10 Domin Saka CCTV A Kano

GANDUJE

Wata Babbar Kotun Taraiyya Mai zamanta a nan Kano, Karkashin Mai Shari’a, A M Liman, Ta Dakatar da Gwamnatin jihar Kano daga Yunkurin Karbo Bashin naira Milyan Dubu 10 domin siyowa da kuma saka Kyamarorin tsaro na CCTV a fadin jihar Kano.

 

Yanke Hukuncin Ya biyo bayan wata kara da Wata Kungiya mai SUNA Kano First Forum KFF ta shigar a  gaban kotun, inda ta bukaci a dakatar da matakin da gwamnatin Abdullahi Umar Ganduje ke yunkurin dauka na karbo lamunin.

 

Sauran wadanda ake kara sun hada da Kwamishinan  Shari’a na Jihar Kano, Sai Kwamishinann Kudi  da  Yan Majalisar  Dokokin Jihar Kano Sai Bankin Access da Ma’aikatar   Kudi  da Kuma Ofishin Ciwo Basussuka na kasa.

 

Wakilinmu Ado Danladi Faringida Ya ruwaito cewa, kungiyar ta KFF, na Kalubalantar Matakin da gwamnatin jihar Kano ke yin a karbo Lamunin naira Bilyan 10 , sakamakon rashin bin ka’idojin da suka shafi karbo bashi.