On Air Now

Off Air

Midnight - 5:00am

Kotu Ta Hana Gwamnan Kano Kama Alhasan Doguwa

DOGUWA DA ABBA GIDA GIDA

Wata babbar kotun taraiyya dake zamanta a Abuja ta hana gwamnan jihar kano, Abba Kabir Yusuf daukar kowane irin mataki na kamawa ko tsare, Dan majalisar wakilai na kananan hukumomin Doguwa da Tudun Wada, Alhasan Ado Doguwa,har sai bayan kotun ta kammala zaman karar da aka shigar gabanta.

Mai shari’a  Donatus  Okorowo shi ne  ya bada  wannan umarni  biyo bayan bukatar da Lauyan Alhasan Ado Doguwa, Afam Osigwe  SAN ya shigar  gaban kotun.

Lauyan Alhasan Ado Doguwa  ya shigar da kara gaban kotun,Yana neman ta baiwa  dan majalisar kariya,  saboda  zargin  gwamnatin kano da  yunkurin sawa a kama  shi  tare da tsare, bisa  zargin da ake masa  da hannu  wajen  tada  zauni tsaye a zaben  shugaban kasa  dana  ‘yan majalisar dokokin taraiyya.

Mai shari’a Okorowa  ya umarci dukkanin bangarorin biyu da kowa  ya tsaya  kan matsayinsa cak, har zuwa  lokacin da kotun  zata  kammala zamanta akan shari’ar.