On Air Now

Off Air

Midnight - 5:00am

Kotu Ta Hana Iyorchia Cigaba Aiyana Kansa A Matsayin Shugaban Jam'iyyar PDP

Sanata Ayu

Wata babbar kotun jihar Benue dake zamanta a birnin Makurdi, Ta haramtawa shugaban jam’iyyar PDP na kasa Sanata Iyorchia Ayu, Cigaba da baiyana kansa a matsayin shugaban jam’iyyar PDP na kasa.

Daukar matakin ya biyo bayan wata kara  da aka shigar  gaban kotun akan shugaban jam’iyyar PDP  na kasa, Inda kuma kotun ta dage zamanta zuwa ranar 17 ga watan gobe  domin cigaba da zaman shari’ar.

Da yake yiwa manema Labarai  jawabi a birnin Makurdi, Mai  shigar da karar, Mister Terhinde Utaan,Ya ce  saboda matakin da shugabannin jam’iyyar  PDP a mazabar  shugaban jam’iyyar  suka dauka na dakatar dashi,  ba  daidai  ba ne  ya  cigaba da  rike  matsayin shugabancin jam’iyyar, wanda hakan zai haddasa samun  rashin hadin kai a tsakanin jam’iyyar.