On Air Now

ZANGON MARAICEN LAHADI

6:00pm - Midnight

Kotu Ta Mallakawa Hukumar EFCC Gidajen Bandirawo Da Amana City Mallakin 'Yan Fansho

BANDIRAW CITY

Kotu ta baiwa Hukumar yaki da masu yiwa tattalin arzikin kasa zagon kasa EFCC damar mallake wasu gine-gine har guda 324 mallakin hukumar fansho ta jihar Kano.

Mai shari’a Inyang  Ekwo  na  babbar  kotun taraiyya dake Abuja  shi  ne ya bada umarnin mallake  gine-ginen.  ga hukumar  EFCC,kamar  yadda  kakakinta  Wilson Uwujaren  ya  baiyaan ta cikin wata  sanarwa  da aka fitar  a ranar  Laraba.

Kadarorin dai sun kunshi  rukunin  gidaje na sheik Jafar Mahmud Adam guda 168  wanda  aka  fi sani da   Bandirawo City  da  Sheik Nasiru Kabara wanda aka fi sani da Amana City  sai  kuma  rukunin gidaje  na sheik   Khalifa  Ishaq  Rabiu  city.

Idan ba’a manta  ba,Yan fansho sun zargi tsohon gwamnan jihar kano Rabiu Musa Kwankwaso  da yin amfani da kudinsu wajen gina  gidajen.