Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja ta tsige shugabannin jam’iyyar ADC karkashin jagorancin Sanata David Mark, tare da soke dukkan matakan da suka dauka a madadin jam’iyyar.
Matakan da shugabancin jam'iyyar a karkashin jagorancin David Mark suka dauka sun hada da tsayar da tsohon mataimakin shugaban kasa, Alhaji Atiku Abubakar, a matsayin dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar a babban zaben shekarar 2027.
Atiku, wanda hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa (INEC) ta riga ta wallafa sunansa a matsayin dan takarar shugaban kasa, ya kuma zabi tsohon gwamnan jihar Rivers, Rotimi Amaechi, a matsayin mataimakinsa.
Sai dai, a hukuncin da ya yanke ranar Alhamis, Mai shari’a Peter Lifu ya ayyana kwamitin rikon kwarya na ADC karkashin jagorancin Sanata Mark a matsayin wanda bai halatta ba, inda ya ce kwamitin ne ya shirya zaben fidda gwani da ya samar da Atiku a matsayin dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar.
Kotun ta amince da hujjojin karar da tsohon mataimakin shugaban jam’iyyar na kasa mai kula da shiyyar Arewa maso Gabas, Nafiu Bala Gombe, ya shigar.
Gombe ya garzaya kotu ne domin kalubalantar tsarin da kwamitin karkashin jagorancin Sanata Mark ya bi wajen karbe ragamar shugabancin jam’iyyar.
Ya bayyana cewa, bayan murabus din tsohon shugaban jam’iyyar na kasa, Cif Ralph Nwosu, shi ne ya cancanci ya karbi ragamar shugabancin ADC.
Saboda haka, ya roki kotun da ta soke dukkan matakan da shugabancin karkashin jagorancin Sanata Mark ya dauka a madadin jam’iyyar, da sauran bukatu.
Wadanda aka shigar da kara a kansu a cikin karar mai lamba FHC/ABJ/CS/1819/2025 sun hada da jam’iyyar ADC, hukumar INEC, Sanata Mark, Ogbeni Rauf Aregbesola da Cif Ralph Nwosu.
Mai karar ya kuma bukaci kotun da ta hana Sanata Mark da Aregbesola cigaba da gabatar da kansu a matsayin shugaban jam’iyyar da sakataren jam’iyyar na kasa, yana mai cewa yadda suka samu mukaman ya saba wa kundin tsarin mulkin jam’iyyar da kuma tanade-tanaden dokar zabe.
Kotun ta amince da bukatun mai karar, tare da bayar da umarnin da ya nema. Hukuncin na iya haifar da jerin sauye-sauye a fagen siyasar kasar, yayin da aka sanya ranar 16 ga watan Janairun 2027 domin gudanar da zaben shugaban kasa.
Tuni dai jam’iyyar ADC ta sha alwashin daukaka kara kan hukuncin.
Da yake mayar da martani kan hukuncin, Sakataren Jin Dadin Jama’a na jam’iyyar ADC na kasa, Mista Nkemakolam Ukandu, wanda daga baya aka shigar da shi cikin karar a matsayin mai ruwa da tsaki, ya ce za su kalubalanci hukuncin a kotun daukaka kara.
Wannan na zuwa ne kasa da sa’o’i 24 bayan dan takarar jam’iyyar, Atiku, ya gudanar da babban gangamin yakin neman zabe a jihar Sokoto, a wani bangare na shirye-shiryensa na takarar shugaban kasa a zaben 2027.
Comments
Add a comment