On Air Now

ZANGON RANA

10:00am - 3:00pm

Kotu Ta Sauke Wani Sanata Daga Kujerarsa.

SANATA ISA

Kotun sauraren kararrakin zabe dake zamanta a birnin Lokoja, Ta sauke shugaban kwamitin majalisar dattawa mai kula da aiyukan hukumar hana fasa kwauri ta kasa, Sanata Jibrin Isah daga kan kujerarsa ta sanata, Bayan data soke sakamakon zabe na rumfunan zabe 94 da suke a shiyyar da yake wakilta.

A yanzu haka mai shari’a K.A Orjiako, Ya umarci hukumar zabe ta kasa  ta gaggauta janye shaidar cin zabe  data baiwa sanatan, Sannan ta  sake gudanar da zaben cike  gibi a rumfunan zabe  da abun  ya shafa.

Dan takarar  jam’iyyar  PDP, Dr  Victor  Adoji  ne  ya shigar da kara  gaban kotun, inda  yake  kalubalantar  nasarar da  Sanata Isah ya samu, bisa ikirarin cewar  an soke sakamakon zabe  a  wasu akwatinan  zabe  da aka samu aringizon  masu kada kuri’a.

A hukuncin da alkalin kotun ya yanke  ya amince da dukkanin wasu shaidu da  mai kara  ya shigar gaban kotun.

Sanata Isa  dan shekara  63 a duniya  ya kasance  tsohon dan siyasa, Kuma  shine  wanda aka  gani  ya  durkusawa  Gwamna  Yahya Bello na jihar Kogi  ya bashi hakuri, kamar yadda aka nadi bidiyon nasa  ta cikin wata  kyamara.