On Air Now

ZANGON RANAR ASABAR

Noon - 6:00pm

Kotu Ta Soke Takarar Sanata Godswill Akpabio

SANATA GODSWILL AKPABIO

Reshen wata kotun daukaka Kara dake zamanta a Abuja, ta jingine hukuncin da wata babbar kotun taraiyya tayi, wanda ta aiyana Sanata Godswill Akpabio a matsayin halastaccen dan takarar sanatan Akwa Ibom ta Arewa karkashin jam’iyyar APC.

Kotun mai Alkalai Ukku, Mai shari’a Danlami Senchi ne ya karanta hukuncin da kotun ta yanke a ranar Litinin, Inda  ya baiyana cewa, Sanata Godswill Akpabio, ya gaza gabatar da kwararan hujjojin da suka dace kan kasancewarsa a matsayin, bisa  ga tanadin doka.

A saboda haka ne, Alkalan kotun suka baiyana cewa, Kasancewar Godswill Akpabio ya nemi zama dan takarar shugabancin kasar nan karkashin jam’iyyar  APC, bai samu  damar shiga zaben fidda gwani na kujerar Sanatan Akwa Ibom ta Arewa ba, wanda hukumar Zabe ta kasa ta sanya ido a kansa ranar 27 ga watan Mayun Bana, kuma har ta kaiga an aiyana Udom Ekpoudom a matsayin wanda ya lashe zaben.

Kotun daukakar karar, ta jingine hukuncin da babbar kotun  taraiyyar dake zamanta a Abuja tayi a ranar 22 ga watan Satumbar  da  ya  gabata,  inda  ta bukaci  hukumar  INEC  ta  gaggauta  saka  Akpabio a matsayin halastacen  dan takarar sanatan  Akwa Ibom ta arewa a karkashin jam’iyyar  APC.