On Air Now

Maraicen Asabar

6:00pm - Midnight

Kotu Ta Tsawaita Umarnin Hana Dakatarwa Ko Korar Wike Daga Jam'iyyar PDP

Babbar kotun tarayya da ke Abuja, ta tsawaita wa’adin umarnin hana jam’iyyar PDP dakatarwa ko korar Gwamna Wike na jihar Rivers daga jam’iyyar.

Wannan umarni dai yana jiran sauraron karar da gwamna Wike ya shigar a kan jam’iyyar PDP.

Mai shari’a James Omotosho, ya bayar da umarnin tsawaita wa’adin ranar 2 ga watan Fabrairu, jim kadan bayan sanya ranar 6 ga watan Maris, domin sauraren duk wata kara da ta shafi shari’ar.

Gwamna Wike dai ya shigar da karar ne a gaban kotu, inda ya koka da barazanar da shugabannin jam’iyyar PDP ke yi na dakatar da shi ko kuma su korabaki daya.