On Air Now

ZANGON MARAICE

3:00pm - 8:00pm

Kotu Ta Yankewa Mutane 3 Hukuncin Kisa A Jihar Jigawa

Wata Kotu a jihar Jigawa ta zartas da hukuncin kisa ta hanyar rataya ga wasu mutane 3 da aka samu da aikata muggan laifuka da suka hadar da  kisan kai da  garkuwa da mutane da kuma fashi da makami ta hanyar amfani da manyan bindigogi.

Shaidu 5 ne suka tabbatar da aikata laifukan mutanen 3 sai dai  kotun ta wanke mutum na 4 Ya’u mai Hatsi wanda aka gaza samunsa da laifin da ake zargi.

Kotun wadda ta yi zama a karamar hukumar Kaugama ta samu Suleiman Bello da Auwalu Muhammad da kuma Yakubu Muhammad da tarin laifukan, ciki har da garkuwa da wata mata Hadiza Abdullahi da ke garin Marma a karamar hukumar Kirikasamma tare da neman biyan fansar naira miliyan 150.

Har Ila yau,   yayin zaman shari’ar mutanen 3 sun kuma amsa laifinsu na kisan wani magidanci Audu Saje a karamar hukumar ta Kaugama.

Yayin sumamen da jami’an tsaro suka kai gidan mutanen 3 sun sanar da samun bindigogi kirar AK-47 guda 3 da wata babbar bindiga kirar GPMG sai carbin harsasai guda 9 kana harsasai na daban 309 sai kuma tsabar kudi Naira miliyan 2 da dubu 70 baya ga mashin wanda aka yi ittifakin na mutumin da suka kashe ne Audu Saje.