On Air Now

ZANGON MARAICE

3:00pm - 8:00pm

Kotu Ta Yankewa Wani Dan Takarar Gwamna Hukuncin Zaman Gidan Kaso Na Shekara 42

Bassey

Wata Babbar kotun taraiyya dake zamanta a Akwa Ibom, ta yankewa dan takarar gwamnan jihar a karkashin jam’iyyar YPP, Bassey Albert hukuncin zaman gidan gyaran hali na tsawon shekara 42, sakamakon aikata lefin Damfara.

A shekarar  2019 ne, Hukumar EFCC ta gurfanar da Albert gaban kotun bisa tuhumarsa da aikata lefuka shida, inda ta zarge shi da mallaka wasu motoci  shida akan kudi naira milyan 204 a lokacin da yake  kwamishinan kudi na jihar.

A hukuncin data yanke, Mai shari’a Agatha Okeke, ta samu  dan takarar gwamnan kuma sanatan Akwa Ibom ta Arewa maso gabas da aikata lefukan, sannan kuma ta aike dashi zuwa gidan gyaran hali na Ikot Ekpene.

A baya Albert  ya kasance dan jam’iyyar PDP kafin ya sauya sheka zuwa jam’iyyar  YPP, inda ya samu tikitin takarar kujerar gwamnan  jihar  a zabe mai zuwa.