On Air Now

ZANGON RANA

10:00am - 3:00pm

Kotu Ta Yankewa Wani 'Dansanda Hukuncin kisa Ta Hanyar Rataya

police

Babbar kotun birnin Fatakwal dake jihar Rivers, Ta yankewa wani korarren dan sandan mai suna James Imhalu, hukuncin kisa ta hanyar rataya, bayan kisan wani matukin motar haya a shekarar 2015, bisa ya ki bashi cin hancin naira 100.

Mai shari’a Elsie Thompson yayin yanke hukuncin, Tace hujjojin da aka gabatarwa da kotun tun da fari, su suka sa aka kori jami’in daga aiki, sakamakon yana sane ya aikata kisan matukin mai suna Legbara David, a shataletalen  dake birnin na Fatakwal.

Kazalika mai shari’a Thompson, ta bayyana abinda  Imhalu ya aikata matsayin wanda ya saba da tsarin kasancewar jami’an yansanda  a cikin al’umma.

Daya daga cikin lauyoyin masu karar Kingsley Briggs, yace hukuncin zai zage radadi ga iyalan mamacin.