On Air Now

ZANGON MARAICE

3:00pm - 8:00pm

Kotu Ta Yankewa Wasu Mutane 3 Hukuncin Kisa Saboda Satar Cajar Waya

Wata babbar kotun jihar Ekiti da ke zamanta a birnin Ado Ekiti ta yanke wa wasu mutane uku hukuncin kisa ta hanyar rataya bisa samun su da laifin hada baki da kuma fashi da makami.

Wadanda aka  yankewa  hukuncin sun hada  da  Omotayo Deji  da Chidiebere Ifeanyin da  kuma  Bolaji Usman, inda aka gurfanar da su a gaban mai shari’a Bamidele Omotoso a ranar 21 ga watan Janairun 2020, bisa tuhume tuhume hudu.

A bayanin da ya yi wa ‘yan sanda, Daya daga cikin mutanen da aka  yiwa fashi da makamin,  Ya  ce  mutanen sun afka masu da sara  da adduna da sauran wasu makamai, inda suka karbe masu wayoyinsu na hannu da  Na’ura mai kwakwalwa  kirar  tafi da gidanka, sai  Caja da  kum  na’urar yin cajin waya.

A hukuncin da ya yanke, Mai shari’a Bamidele Omotoso, Ya yanke masu hukuncin kisa  ta hanya.