On Air Now

Off Air

Midnight - 5:00am

Kotu Ta yi Watsi da Bukatar Belin Nnamdi Kanu Jagoran IPOP

Babbar kotun tarayya da ke Abuja ta yi watsi da bukatar bayar da belin shugaban haramtacciyar kungiyar 'yan aware ta Biyafara, IPOB, Nnamdi Kanu.

Da take yanke hukuncin a yau Talata, Mai shari'a Binta Nyako, ta ce bukatar tamkar cin zarafi ne ga shari'a, kuma yunkuri ne na ci gaba da magana a kan abin da aka riga aka yanke hukunci a kai.

Sai dai ta shawarci wanda ke neman belin da ya nufi kotun daukaka kara a kan batun, idan bai gamsu da hukuncin ta ba.

Mai shari'ar ta ce tun bayan da aka yanke hukunci a watan Yuli na 2017, lokacin da aka bayar da belin Kanu zuwa yau, an daga shari'ar har sau 15, kuma har yanzu ba a kai ga sauraren ainahin shari'ar tasa ba ma.

Ta kara da cewa ba ta gamsu da dalilan da jagoran na IPOB din yake bayarwa ba na kin bayyana a kotu domin ci gaba da shari'arsa.

Dangane da batun korafin rashin yi masa adalci, Mai Shari'a Nyako ta ce daga bayanan kotun, lauyoyin Kanu na wakiltarsa tun daga ranar da aka soke belinsa, haka ma wadanda suka tsaya masa, kuma ba wani lokaci da aka ki yi masa adalci a shari'ar.

Mai shari'ar ta ce idan har yana son a sake ba shi beli to sai ya yi wa kotu cikakken bayani da zai gamsar da ita kan dalilin da ya sa ya karya ka'idar belin da ta ba shi a baya.

Daga nan sai ta dage sauraren shari'ar zuwa 14 ga watan Nuwamba da kuma jiran sakamakon daukaka karar tasa a kotun daukaka kara.