On Air Now

ZANGON RANA

10:00am - 3:00pm

Kotu Tayi Mi'ara Koma Baya Akan Hana Ganduje Ciwo Bashin Billyan 10 Domin Saka CCTV.

GWAMNA GANDUJE

Wata babbar kotun tarayya dake zamanta a nan Kano, ta yi mi’ara koma baya, akan wani umarnin wucin gadi data bayar a zamanta na baya, wanda ya hana yunkurin gwamnatin jihar Kano, na ciwo bashin tsabar kudi da suka kai naira biliyan 10.

Karar wadda aka shigar ta hannun babban daraktan gamayyar kungiyoyin farar hula,mai suna KFF,  Dr Yusuf Isyaka Rabi'u, Ya bukaci kotun ta dakatar da gwamnatin   jihar kano  ciyo bashin makudan kudaden.

Tunda fari dai, kotun ta hana ciyo bashin, wanda gwamnatin tace zata yi amfani dasu ne wajen sanya kyamarorin tsaro na CCTV domin inganta sha'anin tsaro  a  jihar  nan .

Alkalin kotun, mai shari'a Abdullahi Liman, ya janye umarnin  wucin gadin daya bayar a ranar 1 ga watan Yuli, biyo bayan bukatar da Lauyan wadanda ake kara Muhammad Dahuru yayi, inda ya roki kotun data jingine hukuncinta  na baya  data yi.