On Air Now

ZANGON MARAICE

3:00pm - 8:00pm

Kotu Zata Yankewa Wasu Matasa Biyu Hukunci Kan Bata Sunan Gwamna Ganduje

Mubarak Muhammad da Gwamna Ganduje

An gurfanar da wasu matasa biyu, Mubarak Muhammad da Kuma Nazifi Bala a gaban wata kotun Majistare mai lamba 58 dake nan Kano, bisa zarginsu da bata sunan gwamnan jihar Kano, Dr Abdullahi Umar Ganduje.

A cikin wani faifan  bidiyo da aka wallafa a shafin sada zumunta na facebook, Matasan biyu  sun baiyana   cewa gwamna  Ganduje yana siyar da filayen mutane, sannan kuma  yana yin Likimo, Matasan biyu  sun amsa lefin da ake tuhumarsu  das hi bayan da aka  fara karanta masu abunda ake zarginsu da yi.
Daga nan ne kotun ta dage zamanta zuwa ranar 7 ga watan Nuwambar da muke ciki domin yanke masu  hukunci.

Hukumar tace fina-finai da Dab'i ta jihar kano karkashin Afakallah ce ta  gurfanar da matsan biyu gaban kotu.

More from Labarai