On Air Now

ZANGON RANA

10:00am - 3:00pm

Kotun Koli Ta Tabbatar Da Abba Amatsayin Gwamnan Kano

Kotun kolin Najeriya da ke zamanta a birnin tarayya Abuja ta tabbatar da Alhaji Abba Kabir Yusuf a matsayin zababben gwamnan jihar Kano.

Jam'iyyar APC ta kalubalanci Nasarar Abba Kabir a Zaben Gwamna a 2023 da dan takararta na Gwamna a Kano,  Nasiru Yusuf Gawuna. 

Hukuncin da aka yanke a yau Juma’a ya biyo bayan shafe watanni ana shari'a daga Kotun kararrakim zabe zuwa Kotun daukaka kara da kuma Kotun Koli  tsakanin jam’iyyar NNPP da APC a jihar ta Kano.

Tuni aka tsaurara matakan staro a Jihar gabanin hukuncin.