On Air Now

Off Air

Midnight - 5:00am

Kotun Koli Ta Tabbatar Da Takarar Hajiya Laila Buhari

Hajiya Laila Buhari

A yaune, Kotun koli ta sake tabbatar da Hajiya Laila Buhari a matsayin 'yar takarar sanatan Kano ta tsakiya, a karkashin jam'iyyar PDP a zabe mai zuwa.

Tunda farko  kotun daukaka  kara ce ta  baiyana  Hajiya  Laila Buhari a  matsayin 'yar  takarar  sanatan  Kano  ta tsakiya  a karkashin jam'iyyar PDP, inda  ta  soke  zaben  da aka yiwa  Danburan Nuhu.

A  hukuncin   da  Kotun kolin ta yanke  karkashin mai shari'a  Muhammad Lawal Garba, Ta kori  karar  da Nuhu  Danburam  Abubakar ya shigar  a gaban ta.

Mai shari'a  Muhammad Lawal  yana tare da Mai shari'a  Kudirat Kekere Ekun da Alkali  Saulawa  Sai mai shari'a Ibrahim Jauro da Alkali  Emmanuel  Agim a zaman kotun da aka yi.