On Air Now

Off Air

Midnight - Noon

Kotun Koli Za Ta Yanke Hukunci Kan Karar Zaben Gwamnan Jihar Osun

Jam’iyyun APC da PDP a jihar Osun sun baiyana fatan samun nasara a yayin da Kotun Koli zata aiyana halastaccen wanda ya lashe zaben gwamnan jihar da aka yi ranar 16 ga watan Yulin bara, A yau Talata.

Idan ba’a  manta  ba, A  hukuncin da kotun sauraren kararrakin zaben  gwamnan jihar  ta yanke  ranar  27 ga watan   janairun bana, karkashin mai shari’a  Tertse Kume,  Ta soke  nasarar  da gwamna  Adeleke  na  jam’iyyar  PDP  ya samu  tare da aiyan tsohon gwamnan jihar  Oyetola  na jam’iyyar APC  a matsayin wanda  ya lashe  zaben gwamnan jihar  da aka yi.

Sai dai saboda rashin gamsuwa da hukuncin ne,  Gwamna Adeleke  tare da jam’iyyarsa ta PDP, garzayawa  gaban kotun  daukaka  kara, Wanda a ranar  24 ga watan  Maris  din bana  ne  kotun ta  soke  hukuncin da kotun baya  ta yanke,Tare  da sake  tabbatar da Adeleke a matsayin wanda  ya samu nasara.

A  mabanbantan hirar  da suka yi da manema Labarai  gabanin hukuncin na  yau da za’a yanke, kakakin jam’iyyar  APC  a jihar Kola Olabisi, da kuma takwaransa na jam’iyyar  PDP Oladele Olabamiji, Kowannensu  ya baiyana fatan  cewar  tsaginsu ne zai samu nasara.