On Air Now

Off Air

Midnight - 5:00am

Kotun Kolin Amurika Ta amincewa Amurikawa Yin Amfani da Bindiga A Bainar Jama’a.

AMERICAN SUPREM COURT

A Ranar Alhamis ne Kotun kolin Amurka ta yanke hukuncin cewa, Amurkawa na da yanci na rike bindiga a biyanar jama’a, Wannan hukunci na zuwa ne makonni bayan wani kazamin harin bindiga da aka kai a makaranta.

Hukuncin ya ci karo da dokar da birnin New York   ya saka, wanda  ke bukatar mutum ya yi cikakken bayani akan cewar yana da yancin mallakar bindiga  domin kare kansa, kafin samun lasisin mallakar  bindigar.

Duk da kiraye-kirayen da ake ta yi na kayyade amfani da bindigogi bayan jerin  harin  bindiga  biyu da aka samu a  watan Mayu, kotun ta goyi bayan masu fafutuka da suka ce kundin tsarin mulkin Amurka ya ba da damar mallakar bindigogi da kuma daukar makamai.

Hukuncin shine na farko da kotu ta yanke a  cikin  shekaru goma da aka kwashe  ana  dambarwa kan amfani da makami a kasar.