Kotun Tafi-da-Gidanka ta REMASAB Ta Hukunta Total Energies, MRS, A.A. Rano da Sauran Masu Laifin Keta Dokokin Tsaftar Muhalli.
Hukumar Kwashe Shara da Tsaftar Muhalli ta Jihar Kano (REMASAB) ta ci gaba da ƙarfafa aiwatar da dokokin tsaftar muhalli, inda Kotun Tafi-da-Gidanka ta Muhalli da take gudanar da zamanta na mako-mako ta gurfanar tare da hukunta kamfanoni da masu gidaje da dama bisa laifukan karya dokokin tsaftar muhalli a sassa daban-daban na Jihar Kano.
A yayin atisayen tabbatar da bin doka da aka gudanar a kan titin Civic Centre da Gwarzo Road, Kotun ta samu Total Energies Filling Station da ke Civic Centre da laifuffuka da suka haɗa da zubar da shara ba bisa ƙa'ida ba, ciyayi masu yawa, fitsari a fili, toshe magudanan ruwa, zubar da shara a muhalli, rashin tsaftar muhalli, lalacewar rijiyar duba magudanar ruwa, da kuma rashin wadatattun kwantena na zubar da shara. Kotun ta yanke wa kamfanin hukuncin zaman gidan yari na makonni biyu ko kuma biyan tara.
A cikin sanarwar da mai magana da yawun hukumar ta REMASAB, Abubakar Ahmad ya sanyawa hannu, kotun ta samu MRS Filling Station da laifin barin ciyayi masu yawa, rashin kula da bandakuna yadda ya kamata, da kuma fitsari a fili. An yanke wa kamfanin hukuncin zaman gidan yari na makonni biyu ko kuma biyan tara.
Kotun ta kuma bayar da umarnin rufe gidan zama mallakin Usman Abdullahi Tal'udu, bayan an tabbatar da cewa gidan na haifar da wari mai muni, rashin tsaftar muhalli, zubar da shara a ko'ina, da kuma rashin samar da kwantenar zubar da shara.
Haka nan, an samu MH Gano da ke kan titin Gwarzo da laifin rashin tsaftar muhalli, ciyayi masu yawa, bayan gida a fili, da kuma rashin kwantenan zubar da shara. Kotun ta yanke masa hukuncin zaman gidan yari na mako guda ko kuma biyan tara.
Kotun ta kuma hukunta gidan mai na Aliko da ke kan titin Gwarzo bisa laifin barin ciyayi masu yawa, zubar da shara a muhalli, lalacewar rijiyoyin duba magudanan ruwa, ƙofofi masu tsatsa, da kuma rashin tsaftar muhalli. An yanke wa kamfanin hukuncin zaman gidan yari na makonni biyu ko kuma biyan tara.
Bugu da ƙari, Kotun ta bayar da umarnin rufe MYMS Filling Station da ke Gwarzo Road bayan an same shi da laifin toshe magudanan ruwa, barin ciyayi masu yawa, tara kayan da ba a buƙata a kusa da ɗakin janareta, zubar da shara a muhalli, rashin kwantenan shara, da kuma rashin tsaftar muhalli.
An kuma samu gidan mai na A.A. Rano da laifin zubar da shara ba bisa ƙa'ida ba, toshe magudanan ruwa, rashin kula da bandakuna, rashin wadatattun kwantenan shara, zubar da shara a muhalli, da kuma rashin tsaftar muhalli. Kotun ta yanke mata hukuncin zaman gidan yari na kwanaki goma (10) ko kuma biyan tara.
Haka kuma, MMD Oil and Gas shima ya gurfana a gaban Kotun inda aka same shi da laifin lalacewar mashigar harabar kamfanin, barin ciyayi masu yawa, zubar da shara ba bisa ƙa'ida ba, zubar da shara a muhalli, da kuma rashin tsaftar muhalli. Kotun ta yanke mata hukuncin zaman gidan yari na kwanaki goma (10) ko kuma biyan tara.
Da yake jawabi bayan kammala shari'o'in, Manajan Daraktan REMASAB, Dr. Muhammad S. Khalil, ya sake jaddada ƙudirin Hukumar na cigaba da aiwatar da dokokin tsaftar muhalli a faɗin Jihar Kano.
Ya yi kira ga mazauna jihar, kamfanoni masu zaman kansu, cibiyoyin kasuwanci da sauran masu ruwa da tsaki da su tabbatar da tsaftar muhallansu tare da bin dukkan ƙa'idojin tsaftar muhalli, yana mai gargaɗin cewa duk wanda aka samu da laifin karya dokokin tsaftar muhalli zai fuskanci hukuncin da doka ta tanada ba tare da nuna bambanci ba.
Comments
Add a comment