On Air Now

ZANGON MARAICE

3:00pm - 8:00pm

Guda Cikin Yan Najeriya Hudu na Fama da Larurar Kwakwalwa - Kiyawa

Dr. Ali Kiyawa

Shin ka san cewa ana kiyasin ɗaya cikin kowane mutum huɗu a Najeriya na rayuwa da wata matsalar lafiyar ƙwaƙwalwa?

Wannan ƙididdiga ta samo asali ne daga wasu bayanai da ɗan majalisar dokokin Kano, Dakta Ali Kiyawa, ya yi, inda ya ce hakan na nuna muhimmancin ƙara ƙarfafa ayyukan kula da lafiyar ƙwaƙwalwa a ƙasar nan.

Ɗan majalisar mai wakiltar mazabun Bagwai da Shanono ya bayyana hakan ne yayin da yake gabatar da wani kudiri da ke kira ga Gwamnatin Jihar Kano da ta kafa asibitocin kula da lafiyar ƙwaƙwalwa guda uku a shiyyoyi daban-daban, domin faɗaɗa damar samun ingantaccen kulawar kwakwalwa a jihar.

Da yake zantawa da Arewa Radio a wani sakon murya da ya aiko ta dandalin sada zumunta na WhatsApp, Dakta Ali Kiyawa ya ce buƙatar hakan ta taso ne bayan da aka miƙa Asibitin Kula da Lafiyar Ƙwaƙwalwa na Tarayya da ke Dawanau ga gwamnatin tarayya, lamarin da ya bar Jihar Kano da cibiyoyi uku kacal masu kula da lafiyar ƙwaƙwalwa a cikin asibitocin gwamnati domin yi wa al'ummar jihar hidima.

Ya ce kafa keɓaɓɓun asibitocin kula da lafiyar ƙwaƙwalwa zai ƙara yawan mutanen da za su samu kulawar ƙwararru, ya sauƙaƙa gano cututtukan tun da wuri da fara magani cikin lokaci, tare da rage cunkoson da ake fuskanta a cibiyoyin da ake da su yanzu.

Dakta Ali Kiyawa ya kuma bayyana cewa inganta kula da lafiyar ƙwaƙwalwa na iya taimakawa wajen rage laifuffukan da ke da alaƙa da matsalolin ƙwaƙwalwa da kuma shaye-shayen miyagun ƙwayoyi, yana mai jaddada cewa gano matsalolin da wuri da kuma ba da kulawar gyaran hali suna da matuƙar muhimmanci wajen kare lafiyar al'umma da inganta zaman lafiya.

Comments

Add a comment

Log in to the club or enter your details below.

A Biyo Mu a Shafukan Sada Zumunta

Today's Weather

  • Kano

    Sunny intervals

    High: 34°C | Low: 22°C