On Air Now

ZANGON RANAR ASABAR

Noon - 6:00pm

Ku Karbi Kudin 'Yan Siyasa Amma Kar Ku Zabe Su Inji Peter Obi

PETER OBI

‘Dan takarar shugabancin kasar nan a karkashin jam’iyyar Labour, Peter Obi, Ya bukaci ‘yan Najeriya dasu rika karbar kudin da ‘yan siyasa ke basu , kasancewar dama tun asali kudinsu ne, amma kuma kada su zabe su a lokacin zabe.

Peter  Obi  ya  yi wannan  roko ne, a  yayin gangamin yakin neman zabensa  shida  da mataimakinsa, Datti Baba  Ahmed, a  Ilorin babban birnin jihar Kwara.

Ya kara da cewa, ba  ya son Najeriya  ta  kasance a hannun  mutanen  da a lokacinsu a ke samu  Macizai  suna  hadiye  kudi, a saboda  haka  ya kamata  al’ummar kasa su dauki matakin da  ya dace a wannan lokaci.

A  cewar  Peter  Obi, gwamnatinsa  shida  da Baba  Ahmed  zata samar da kyakykyawan yanayi ga matasa, a saboda  haka ne  ma  ya bukace su da su yi kyakykyawan shiri  a  zaben mai zuwa.