On Air Now

ZANGON MARAICE

3:00pm - 8:00pm

Kungiyar ASUU Ta Ce Kakakin Majalisar Wakilai Ya Yaudare Ta

Femi da Osodoke

Majalisar Wakilai taga baiken shugaban kungiyar Malaman Jami’oi ta kasa ASUU, Farfesa Emmanuel Osodeke, bisa ikirarin da yayi na cewar, kakakin zauren majalisar wakilai, Femi Gbajabiamila , ya yaudari malaman jami’oin kasar nan, bayan da yayi uwa da makarbiya wajen ganin sun janye yajin aikin watanni takwas da suka dauki lokaci suna yi.

A wata sanarwa  da  shugaban kwamitin yada labarai  da hulda da jama’a  na majalisar, Benjamin Kalu ya fitar a jiya,  Yana mai cewa babu wani lokaci da aka cimma wata matsaya tsakanin malaman jami’oin da kuma kakakin majalisar akan cewar  za’a biyasu  albashin su na lokacin da suka dauka suna yajin aiki.

Sai dai kuma, a hirarsa  da manema Labarai,  Shugaban Kungiyar ASUU  ya  jaddada  cewar, kungiyar   ta  janye  yajin aikin ta a ranar  14  ga watan October  ne   a  sakamakon alkawuran   da kakakin majalisar wakilai   Femi  Gbajabiamila  yayi masu na cewar  za’a biya su hakkokinsu.