On Air Now

ZANGON MARAICE

3:00pm - 8:00pm

Kungiyar ASUU Ta 'Dora Alhakin Dogon Yajin Aikin Da Take Yi Akan Gwamnatin Taraiyya

BUHARI DA ASUU

Kungiyar Malaman jami’oi ta kasa ta dora alhalkalin dogon yajin aikin da suke yi akan gwamnatin taraiyya da kuma wadanda ba ‘ya’yan kungiyar ba.

A saboda haka ne suka bukaci al’ummar kasar nan, dasu tambayi gwamnatin taraiyya lokacin da zata saka hannu akan  yarjejeniyar kwanan nan da suka cimmawa  a tsakaninsu.

Idan ba’a manta ba, a ranar Litinin ne, Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya bukaci Malaman jami’oin dake yajin aiki  da suyi la’akarin da halin da matasa masu tasowa ke ciki, sannan su koma bakin aiki, yana mai cewar ya kamata ayi adalci  kan cigaba da zaman dirshan da Daliban kasar nan ke yi a gidajensu.

To sai dai a wata zantawa da aka yi dashi, Shugaban Kungiyar ASUU na kasa, Farfesa Emmanuel Osodeke, Ya nemi Yan Najeriya dasu tambayi gwamnati lokacin da zata biya masu bukatunsu.

More from Labarai