On Air Now

ZANGON DARE

8:00pm - Midnight

Kungiyar ASUU Tace Dole Gwamnatin Taraiyya Ta Biya Ta Albashin Watanni Shida, Idan Tana Son Ta Koma Bakin Aiki

ASUU

A yayin da Kungiyar Malaman Jami’oi ta kasa tasha alwashin cigaba da yajin aikin data shafe watanni 6 tana kan yi, har sai an biya ta kudaden ariyas na albashin watanni shida data shafe tana kan yajin aiki.

Kazalika Malaman jami’oin sun baiyana cewa ba zasu  koyar da Dalibai abunda suka rasa na tsawon watanni shida suna yajin aiki ba, idan har gwamnatin taraiyya taki biyansu albashinsu na watanni shida da suka shafe suna yajin aikin.

Shugaban Kungiyar Farfesa Emmanuel  Osodoke  ne ya baiyana haka a daren jiya, lokacin da yake mayar da martani kan kalaman da ministan ilimi Adamu Adamu yayi, Inda yace gwamnati ba zata biya malaman jami’oi albashinsu na tsawon watanni shida  da suka shafe suna yajin aiki.

Osodoke ya kara da cewa ministan  wasa yake yi, Kuma matukar suka ki biyansu albashinsu na tsawon watanni shida, to babu shakka zasu fara bawa dalibai  Lakca ne tsa sabon zangon karatu na shekarar 2022 zuwa  2023, sannan kuma ba zasu  rubutawa daliban jarabawar zangon karshe ba.

A wani bangaren kuma, Ministan Ilimi, Adamu Adamu, ya musanta rahotannin dake cewar shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bashi umarnin kawo karshen  yajin aikin da Malaman Jami’oi na kasar nan ASUU ke yi a cikin makwanni biyu  rak.

Ministan ya baiyanawa manema Labarai na fadar shugaban kasa a jiya cewa shugaban kasar ya fada masa cewa ya warware matsalolin cikin kankanin lokaci, sabanin yadda ministan kwadago da samar da guraben aiki  Chris Ngige ya baiyanawa manema labarai.

Ministan ya kuma bayyana cewa akwai yiyuwar kungiyoyin biyar na jami’o’in su janye yajin aikin da suke yi nan da mako Daya  yayin da har yanzu babu tabbacin da ake dashi akan kungiyar malaman jami’oi ta kasa  ASUU.

Ya kara da cewa, duk da Naira tiriliyan 2 da bilyan 5 da ake kashewa a fannin ilimi ta karkashin asusun  tallafawa manyan makarantu na kasa  TETFUND da kuma na  Hukuamr Ilimin Bai Daya UBEC, Har yanzu  malaman jami’oin  sun dage  kan cigaba da yajin aikin aikin da suke yi, wanda bukatar su sai ta lakume naira tiriliyan 1 da bilyan 2.