On Air Now

ZANGON BARKA DA SAFIYA

5:00am - 10:00am

Kungiyar Dalibai Ta Yabawa Gwamnati Kan Cire Manyan Makarantu Daga Tsarin Biyan Albashi Na IPPIS

Gwamnatin tarayya ta cire manyan makarantun kasar nan daga cikin tsarin na biyan albashin bai daya mai taken (IPPIS) ba tare da bata wani lokaci ba.

Haka kuma an umurci Jami’o’in kasar nan  da su fara daukar ma’aikatan  da suke bukata,  ba tare da neman wani izini  daga   ofishin shugabar ma’aikata  ta kasa ba,  domin a rage yawan wahalhalun da ake fuskanta a  bangaren ilimi.

Ministan Ilimi, Farfesa Tahir Mamman  ne  ya bayyana haka a karshen taron majalisar zartarwa  na kasa  da aka gudanar  jiya  a Abuja, inda ya ce an dauki matakin ne domin rage kalubalen da ke fuskantar manyan makarantun kasar nan.

A wani bangaren kuma,  , Ministan yada labarai, Mohammed Idris, ya bayyana cewa, taron majalisar zartarwa  na kasa   ya  amince da sake  duba bangarorin  da  hukumar  hana fasa  kwauri  ta kasa  ta daukewa  biyan haraji,  domin magance matsalar  zurarewar  kudaden shiga da ake samu.

Nan kuma, kungiyar dalibai ta kasa NANS, ta yabawa gwamnatin tarayya bisa yadda ta cire manyan makarantun kasar nan  da ga cikin tsarin biyan albashi na  IPPIS.

Kungiyar  ta  ce  matakin zai kawo karshen wani bangare na rashin jituwa da ake  yawan samu  daga  bangarorin.

A wata sanarwa da shugaban majalisar kolin kungiyar  na kasa,  Kwamared Akinteye Afeez ya fitar a daren jiya, ya ce matakin  zai saukaka  yanayin gudanar da al’amura a  makarantun kasar nan.