On Air Now

ZANGON DARE

8:00pm - Midnight

Kungiyar IPMAN Ta Ce Farashin Litar Mai Ba Zai Yi Kasa Da Naira 500 Ba

MAN FETIR

kungiyar dillalan man fetur ta kasa mai zaman kanta IPMAN, ta ce sabon farashin Litar man fetur ba zai iya kasa da naira 500 ba.

Mukaddashin shugaban kungiyar IPMAN, Zarama Mustapha, ya bayyana cewa kamfanin mai na kasa  NNPC, shi ne  kadai  zai  iya  kayyade farashin da  kowanne  dillalin  mai a kasar  nan  zai iya siyar  das hi, kasancewar  kanfanin shi kadai ya  ke shigo da tacaccen mai.

A cewarsa, Yanzu haka dillalan man su  kara farashin  litar  mai sama da naira  460 a rumubunan ajiyar mai  na masu zaman kansu,  wanda  hakan  zai  a kara samun tashin farashin saboda  biya masa kudin dako da  sauran dawainiyar  da za’a yi masa.