On Air Now

Off Air

Midnight - Noon

Kungiyar IPOB Ce Ke Fasa Bututan Mai

Shugaban Kasa Muhammadu Buhari Ya zargi Kungiyar ‘Yan Aware ta IPOB da laifin fasa bututan Mai da Sauran kayayyakin amfanin Yau da Kullum.

A yayin hirarsa da jaridar  Bloomberg,  Shugaba Buhari ya koka kan yadda  lefukan da kungiyar ke aikatawa  suka kawo nakasu wajen aiyukan hako albarkatun mai a kasar nan, Sai dai kuma yace an dauki dukkanin wasu matakai da suka dace domin  dakile lefukan  satar Danyen Mai da kuma Fasa Bututan Mai.

Kazalika yace, A  Bara gwamnatinsa ta fara yunkurin cire tallafin Mai, amma daga bisani  ta gano  cewa  yunkurin  bai dace ba.

Da yake mayar da martani game da zargin da aka yiwa  Kungiyar ta IPOB,  Sakataren Yada Labaranta, Emma Powerful, Ya baiyana ikirarin da shugaban kasar yayi a matsayin abun dariya, Inda ya jaddada  cewa abunda kungiyar tasa gaba shine  tabbatar da samun yancin kasar Biyafara, Ba wani abu can na daban ba.