On Air Now

ZANGON MARAICE

3:00pm - 8:00pm

Kungiyar IPOB Ta Zargi Kotun Koli Da Nuna Son Kai Kan Shari'ar Da Ake Yiwa Jagoranta Nnamdi Kanu

Nnamdi Kanu

Kungiyar Yan Aware ta yankin Kudu maso gabashin kasar nan da aka fi sani da IPOB, Ta nuna bacin ranta kan jan kafar da Kotun Kolin kasar nan ke yi, dangane da daukaka karar da gwamnatin taraiyya ta yi,kan kalubalantar hukuncin da Kotun daukaka kara ta yi na wanke jagoransu, Mazi Nnamdi Kanu.

A wata sanarwa da kakakin kungiyar Emma Powerful  ya fitar, Ya  ce  jinkirin gudanar da shari’ar da ake samu abun damuwa ne.

Kungiyar ta IPOB  ta  baiyana mamakinta kan yadda  Kotun Kolin zata buge da sauraren kararrakin da suka shafi  ‘yan siyasa,amma kuma take nuna halin ko in kula akan shari’ar  jagoran nasu.

Daga karshe kungiyar ta zargi  Kotun kolin kasar  nan da nuna son kai cikin al’amuranta.