On Air Now

Off Air

Midnight - 5:00am

Kungiyar Kwadago Ta Ce Tana Kan Bakanta Na Tafiya Yajin Aiki Matukar Gwamnati Bata Kawo Karshen Matsalar Takardun Kudi

NLC

Kungiyar kwadago ta kasa NLC ta sake jaddada matsayar cewar babu gudu ko ja da baya, kan matakin da zata dauka, na umartar ma’aikatan kasar nan su kauracewa bakin aiki, muddin gwamnatin taraiyya ta gaza kawo karshen matsalar karancin takardun kudi da Man fetir nan da kwanaki bakwai masu zuwa.

Bayanin hakan na kunshe ne ta  cikin wata takardar  bayan taro da kungiyar  ta fitar a ranar Talata, Jim kadan bayan kammala taron kaddamar da kwamitin kolin kungiyar da aka yi  ranar Litinin a Abuja.

Idan ba’a manta ba, Shugaban kungiyar kwadagon ta kasa Joe Ajaero,  ya  fitar  da sanarwar  barazanar  tafiya yajin aiki  na fadin kasa, inda  kuma  ba’a  jima ba ,babban bankin kasa  CBN, Ya umarci daukacin bankunan kasar nan dasu  fara karba  da kumabayar da tsohon kudi.

To sai dai  duk da  wannan  sabon cigaba da aka samu,  Kungiyar kwadagon ta  cikin wata sanarwa  data  fitar,  t ace har  yanzu tana kan bakanta  na  umartar  ma’aikata  su tafi  yajin aiki, Matukar  gwamnatin taraiyya  bata kawo  karshen matsalar  karancin takardun kudi nan da  kwanaki bakwai masu zuwa ba.