On Air Now

Off Air

Midnight - 5:00am

Kungiyar Kwadago Ta Janye Shirinta Na Tafiya Yajin Aiki

Tambarin Tutar NLC

Kungiyar kwadago ta NLC da takwararta ta TUC sun janye aniyarsu ta tafiya yajin aiki daga yau Laraba, domin nuna bacin ransu kan karancin takardun naira da ake samu a kasar nan.

Kungiyoyin biyu  sun baiyana cewar  zasu cigaba da saka ido kan wadatuwar takardun kudin da aka samu a bankunan kasuwanci, kamar yadda  babban bankin kasa  ya bada  tabbacin samuwar  kudin,kafin nan da makwanni biyu masu zuwa  domin sanin mataki  na gaba da zata dauka.

Shugaban kungiyar kwadago ta NLC  Joe Ajaero da takwaransa na TUC  Festus Osifo  ne  suka baiyana haka yayin wani taron manema Labarai na hadin gwiwa da aka shirya a ranar Talata a Abuja, jim kadan bayan kammala  taron kwamitin kolin kungiyoyin na kasa.

Sun baiyana cewar bayan jawabin da suka samu daga majalisun kungiyoyin na jihohi 36 da kuma birnin taraiyya Abuja, Kungiyoyin kwadagon sun cimma matsayar  janye  umarnin da suka fara baiwa  ma’aikata na  yin zaman dirshan a gidajensu.