On Air Now

ZANGON RANA

10:00am - 3:00pm

Kungiyar Kwadago Ta Yi Fatali Da Yunkurin Cefanar Da Kanfanin Samar Da Lantarki Na Kasa

Kungiyar Kwadago ta kalubalanci shirin da gwamnatin tarayya ke yi sake fasalin kamfanin samar da hasken wutar lantarki na kasa.

Idan za a iya tunawa, Gwamnatin Tarayya ta hannun Hukumar  kula da  Kamfanonin Gwamnati ta bayyana shirin sayar da kashi 40 na hannun jarin gwamnati a kamfanonin rarraba wutar lantarki a kasuwar  hada-hadar  jari  ta kasa  a sabuwar  shekara  ta  2024.

A cikin wata  takardar bayan taro  da shugaban kungiyar kwadago ta kasa kwamared  Joe  Ajaero  ya fitar a ranar Talata,  ya ce ‘yan Najeriya sun sha  jin irin wannan labarin  tsawon shekaru da suka gabata,  ba tare da ganin wani kyakykywan  sakamako  ba,  bayan an cefanar  da kadarorin gwamnati  saima  karin wahalhalu  da  tsarin  ke  janyo wa al’ummar Najeriya da tattalin arzikin kasa.

Ya bayyana cewa dalilin da ya sa ake  shirin  sake fasalin  kanfanin samar da hasken lantarkin na kasa  TCN, nada alaka  da  ganin an baiwa  wasu  manyan masu rike da madafun iko,a kasar nan damar karbe ikon tafiyar da harkokin lantarkin a Najeriya domin suci karensu ba bu babbaka.