On Air Now

ZANGON RANA

10:00am - 3:00pm

Kungiyar Kwadago Ta Zargi Gwamnati Da Yin Rufa-rufa Kan Yadda Ake Biyan Tallafin Mai

Tambarin Kungiyar Kwadago

Kungiyar Kwadago ta ta caccaki hukumar kula da harkokin man fetur ta kasa kan yadda ake rufa-rufa wajen biyan kudaden tallafin mai a kasar nan.

Kungiyar ta NLC ta kuma yi zargin  cewa  tsarin cike yake da  almundahana, kamar yadda  ta rubuta  takardar kokenta  ga kwamitin wucin gadi na Majalisar Wakilai da aka domin yin bincike kan yadda ake biyan kudaden tallafin man.

Takardar mai dauke dasa hannun  Shugaban kungiyar kwadago ta  NLC na kasa, kwamaren  Ayuba Wabba, ta yi imanin cewa daya daga cikin manyan dalilan da ke haifar da karuwar farashin man fetur a kasar nan lokaci zuwa lokaci, nada  nasaba  da yadda  sai gwamnati ta shigo da Tacaccen Mai da jama’a zasu yi amfani dashi.

Kungiyar ta kara da cewa, Al’umma da dama  suna tabbacin cewa cire tallafin mai  ga man da ake shigo dashi cikin kasar nan  shine mafita, ta bangaren  bunkasa cigaba a kasar nan.