On Air Now

Off Air

Midnight - Noon

Kungiyar Kwadago zata Yi Zanga-Zanga A Fadin Kasa, Kan Yajin Aikin ASUU.

KUNGIYAR KWADAGO

Kungiyar Kwadago ta kasa ta shirya domin gudanar da wata gagarumar zanga-zanga ta tsawon kwanaki biyu a fadin kasar nan, daga ranar 26 zuwa 27 ga watan da muke ciki, a wani mataki na nuna goyon baya ga yajin aikin da malaman jami’oin kasar nan da sauran wasu kungiyoyi dake makarantun gwamnati ke yi a halin yanzu.

Wata sanarwa dauke dasa hannun shugaban kungiyar na kasa, Kwamared  Ayuba Wabba, da Kuma Babban Sakataren Kungiyar na kasa, Emmanuel Ugboaja,  Tace  za’a  yi zanga-zangar ne a daukacin  jihohin kasar nan, cikinsu hadda Abuja babban birnin taraiyya.

Bugu da kari sanarwar ta baiyana cewa, Za’a fara  zanga-zangar ne daga daukacin  shalkwatocin kungiyar kwadago na jihohi, yayin da Abuja  zanga-zangar  zata  soma  daga  sakatariyar kungiyar kwadago ta kasa.

A wani bangaren kuma, Mai magana da  yawun rundunar yansanda ta kasa, Muyiwa Adejobi ya shawarci wadanda ke shirin gudanar da zanga-zangar dasu sanar da jami’an yansanda, domin  ganin an samar masu da tsaro a lokacin da zasu yi zanga-zangar.

A wani bangaren kuma,Hadaddiyar  Kungiyar Ma’aikatan  Banki Masu Harkokin Inshora  da al’amuran  tafiyar da kudi  ta kasa, Sunce  zasu bi sahun kungiyar kwadago ta kasa wajen  gudanar da zanga-zangar lumana  ta  tsawon kwanaki biyu, domin nuna rashin jin dadinsu  game  da dogon yajin aikin da kungiyar Malaman  jami’oi  ta kasa ke kan yi.

A cikin wata sanarwa mai dauke dasa hannun shugaban kungiyar na kasa Anthony Abakpa da kuma babban Sakataren kungiyar Mohammed  Sheik, wadda aka  fitar a ranar  Lahadi, Tace Yajin aikin wanda  aka fara tun ranar  14 ga watan Fabarairun bana  yakai ma’kura, wanda hakan yasa yake cigaba da gurgunta kwazon dalibai  da haddasa wasu matsaloli.

Daga nan kungiyar tayi kira ga shugaban kasa Muhammadu Buhari, daya  yayi abunda ya kamata domin ganin an kawo karshen yajin aikin da kungiyar ta ASUU ke yi.