On Air Now

Off Air

Midnight - 5:00am

Kungiyar Kwallon Kafa Ta Real Madrid Ta Casa Chelsea Da Ci 2 Da Nema

MADRID

Kwallon da dan wasa Karim Benzema da kuma Marco Asensio suka zura, sun temakawa kungiyar kwallon kafa ta Real Madrid wajen doke Chelsea da ci 2 da nema a wasan daf da na kusa da karshe na gasar cin kofin zakarun Turai, da aka yi a ranar Laraba.

Kungiyar  kwallon kafa ta  Chelsea karkashin  mai horaswarta na rikon kwarya Frank Lampard ta kusa zura kwallo a farkon rabin lokaci amma mai tsaron ragar Madrid Thibaut Courtois ya dakile hare-hare da  Joao Felix da Raheem Sterling  suka rika kaiwa.

A wani bangaren kuma AC Milan ta  samu nasara  akan Napoli da ci 1 tak mai ban haushi.