On Air Now

ZANGON RANA

10:00am - 3:00pm

Kungiyar Likitoci A Najeriya NMA Ta Nesanta Kanta Da Wani Likita Da Ake Zargi Da Sace Kodar Mutum

Kungiyar likitocin ta kasa NMA reshen jihar Plato ta nesanta kanta daga alaka da  Dr Noah Kekere, wanda aka kama bisa zargin satar kodar wata mata.

Idan dai za a iya tunawa, ‘yan sanda sun kama wanda ake zargin ne a garin Jos bayan wani dan kasuwa, Alhaji Kamal, ya zarge shi da cire kodar matarsa a lokacin da aka yi ma ta tiyata a shekarar 2018.

Da yake mayar da martani, shugaban kungiyar NMA a jihar, Dr Bapigaan William Audu, a wata sanarwa da ya fitar, ya ce a binciken da suka yi kan al’amarin, ya nuna cewa  Kekere ba likita ba ne.

A cewar sanarwar, binciken kwakwaf da kungiyar ta yi, ya nuna cewa shi mutum ne mai kwarjini da ke sojan gonad a  nuna cewa shi likita ne.