On Air Now

ZANGON BARKA DA SAFIYA

5:00am - 10:00am

Kungiyar Ma'aikatan Lantarki Ta Kasa Ta Janye Yajin Aikin Data Fara Yi A Ranar Laraba

Ma'aikatan Lantarki

Janyewar ta biyo bayan ganawar da suka yi tsakaninsu da ministan kwadago da samar guraban aikin yi, Dr Chiris Ngige a jiya.

Sanarwar da shugaban Sashin Hulda da jama’a da kuma Yada Labarai na Ma’aikatar kwadago ta kasa  ya  fitar , Ya baiyana cewa an kafa wani kwamiti wanda  zai yi duba na tsanaki kan bukatun da  kungiyar Ma’aikatan Lantarkin ta kasa  domin warware su cikin salama.

Da  yake  tabbatar da janye yajin aikin a daren jiya, Shugaban Kungiyar Ma’aikatan Lantarki ta kasa, Kwamared  Joe Ajero, Yace zasu dakatar da yajin aikin nasu nan da tsawon makwanni biyu kamar yadda suka  kulla yarjejeniya tsakaninsu da  gwamnatin      domin biya masu bukatunsu.

Kazalika yayi fatan gwamnatin taraiyya  zata yi adalci kan matsalolin da suka Dade  suna ci masu tuwo a kwarya  domin magance  su.