On Air Now

Off Air

Midnight - 5:00am

Kungiyar ma'aikatan sufurin jiragen sama ta kasa ta janye yajin aikin gargadi na kwanaki biyu da ta fara

Yajin aikin gargadi na kwanaki biyu da ma'akatan sufurin jiragen sama na kasa suka fara yi ya zo karshe, bayan rokon da suka ce wasu 'yan Najeriya masu kishin kasa sun yi musu

Kungiyar Ma’aikatan Sufurin jiragen sama dake filin jirgin saman Malam Aminu Kano, Sun janye yajin aikin gargadi na tsawon kwanaki 2 da suka yi.

A shekaran jiya ne, Kungiyar  Wadda ke a karkashin hadaddiyar  kungiyar Ma’aikatan Sufurin jiragen sama ta kasa, ta gudanar da wata zanga-zanga bisa zargin gwamnatin Taraiyya  wajen gaza aiwatar da  yarjejeniyar da suka kulla, da kuma  rashin  aiwatar da  sabon mafi karancin  Albashi  kafin   su fara yajin aikin gargadin.

Matakin da suka dauka  ya  gurgunta  yanayin gudnaar da aiyuka  a  Hukumar kula da Sararin samaniya ta kasa NAMA da  kuma Hukumar Kula da Yanayi ta kasa, NiMet, sai kuma  Hukumar Kula da Sufurin Jiragen sama ta kasa NCAA.

A zantawarsa da wakilinmu Victor Chiristopher, Wakilan Kungiyar ta kasa dake a nan kano, a karkashin kwamared Akubo Benjamin, wanda Abdullahi Ibrahim Yayi magana a madadinsa, Yace sun janye yajin aikin ne  biyo bayan rokon da wasu ‘yan Najeriya masu kishin kasa suka yi masu, sakamakon  rashin jin dadin abubuwan da yajin aikin ya haifar.

Kazalika  shima  shugaban kungiyar Kwararrun Ma’aikatan Sufurin jiragen sama ta kasa ANAP reshen jihar Kano, Kwamared  Isa Aliyu, Yayi barazanar  cewar  kungiyar zata dauki matakin tafiya yajin aikin sai Baba ta gani muddin gwamnatin taraiyya ta gaza  biya masu bukatunsu.