On Air Now

ZANGON BARKA DA SAFIYA

5:00am - 10:00am

Kungiyar Matuka Adaidaita Sahu Ta Goyi Bayan Hana Tuka Baburan A Manyan Tititan Birnin Kano

Baburan Adaidaita Sahu

Hadakar kungiyar masu tuka baburan adaidaita sahu ta jihar Kano, ta ce a shirye take tayi biyayya da umarnin da gwamnatin jihar kano ta bayar, na hana tuka Baburan adaidaita sahu a wasu manyan titinan cikin birnin Kano, wanda zai fara aiki daga Gobe Laraba 30 ga watan da muke ciki.

To sai dai kuma  kungiyar  taga baiken matakin da aka dauka a dan takaitaccen lokaci, inda suka yi kira ga hukumomi dasu tsawaita  fara aiki da dokar  a maimakon gobe zuwa wani lokaci na daban.

Shugaban kungiyar, Mansir Tanimu  ne yayi wannan roko a yayin zantawarsa da wakilinmu Abdulmumin Abubakar Tsanyawa da safiyar yau, Inda ya baiyana cewa suna sane da matakin tun lokacin da aka kaddamar da tsarin  sufurin motocin safa-na gwamnatin jihar Kano, amma kuma ba’a sanar dasu sabon matakin b.

Dagan an sai yayi kira ga gwamnatin jihar Kano data samar da isassun Motocin Bas domin saukaka zirga-zirga ga al’ummar jihar Kano, Sannan kuma yaja hankalin yayan kungiyar  dasu yi aiki da umarnin a yayin da zasu yi taron gaggawa na jagororin kungiyar domin tattaunawa kan batun.

Titinan da matakin zai fara  shafa, daga Gobe Laraba, 30 ga watan Nuwambar da muke ciki, sun hada da Titin Ahmadu Bello zuwa Mundubawa da kuma titin zuwa Hadeja sai kuma Tal’udu zuwa kan titin Gwarzo.

Latsa wannan sautin domin jin muryar  tasa.