On Air Now

Off Air

Midnight - 5:00am

Kungiyar Mayakan ISWAP, Ta Dauki Alhakin Harin Da Aka Kai Gidan Gyaran Hali Na Kuje Dake Abuja.

MAYAKAN ISWAP

Kungiyar ISWAP Mai Ikirarin yin Jihadi A Yammacin nahiyar Afrika, Ta dauki alhakin harin da aka kai gidan gyaran hali na kuje dake birnin Taraiyya Abuja a ranar Talata.

Bayanin hakan na a cikin wata sanarwa da kungiyar ta wallafa da harshen Larabci a shafinta  na Amaq dake kan internet.

A yayin da Hukumomin kasar nan suka alakanta harin da  ‘Yan Ta’adda, A yanzu  haka Mayakan Boko Haram 64  cikinsu  hadda  Kwamandojinsu  15  wadanda suka kitsa  harin da aka kai  kan  jirgin kasa a jihar Kaduna, a ranar  28 ga watan Maris din Bana, suna daga cikin  wadanda suka arce daga gidan gyaran halin.

A yayin da  al’umma ke tsaka da yin tir da harin da aka akai, A jiya ne shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya ziyarci  gidan gyaran halin domin  ganin  yadda  harin ya kasance.

Bayan anyi masa bayanin abunda ya faru, Shugaban Kasar ya nuna bacin ransa  ga  jami’an tsaro na sirri dake gidan  gyaran halin wanda yace akwai dimbin ayar tambaya akansu.