On Air Now

ZANGON BARKA DA SAFIYA

5:00am - 10:00am

Kungiyar Miyetti Allah Ta Bukaci Daukar Mataki Kan Wadanda Suka Sare Hannayen Wani Karamin Yaro

Kungiyar Miyetti Allah Kautal Hore ta yi kira ga rundunar yansandan jihar Naija data gagaguta zukole mutanen da datse hannayen wani karamin yaro dan shekara 12 a duniya.

Shugaban kungiyar na kasa, Alhaji Bello Ba’dejo ne ya yi wannan kira a lokacin da ya ziyarci yaron dake kwance a babban Asibitin Karamar hukumar Lapai ta jihar Naija a jiya.

Ba’dejo ya yi kira  ga ‘yan sanda da gwamnatin jihar  data gaggauta  yin bincike  kan cin zalin da aka yiwa yaron  tare da zakulo  wadanda suka aikata danyen aikin.

A baya kakakin rundunar  yansandan jihar Naija  DSP Abiodun Wasiu  ya tabbatar da cewar  wasu mutane da ba’a san ko su waye ba, sune  suka farwa  yaron  tare da sare masa hannayensa a lokacin da shanunsa ke kiwo a kauyen Mayaki dake  karamar hukumar Lapai.