On Air Now

ZANGON BARKA DA SAFIYA

5:00am - 10:00am

Kungiyar NLC Ta Caccaki Tinubu Kan Janye Tallafin Mai

NLC

Kungiyar Kwadago ta NLC ta gargadi shugaban kasa Bola Tinubu da kada ya kuntatawa ‘yan Najeriya biyo bayan kalamansa da ya yi kan cire tallafin man fetur, wanda hakan ya fara haifar da matsalar karancinsa a yanzu haka.

A  wata sanarwa da shugabanta, Comrade Joe Ajaero ya fitar,   Kungiyar  ta baiyana damuwarta  kan  yadda  kalaman  suka  wasu masu gidajen mai suka  rufe  gidajen  mansu, wanda  hakan ya haifar da  tashin farashin man.

Kazalika  ya   bayyana matakin ba tare da  an tuntubi juna ba a matsayin abunda  bai  dace  ba,  Shugaban  kungiyar  ta   NLC ya ce lamarin ya  jefa  jama’a r kasar nan cikin rashin jin dadi, a  maimakon  fatan da suke dashi ga sabuwar  gwamnati.

A  saboda  haka,kungiyar kwadagon ta  shawarci Tinubu da ya  sake  yin tunani  kan manufofinsa  na inganta  tattalin arziki,  domin  temakawa  jama’ar kasa,  maimakon jefa su cikin halin tasku.