On Air Now

ZANGON RANA

10:00am - 3:00pm

Kungiyar SERAP Ta Bukaci Bankin Duniya Ya Dena Bawa Jihohin Kasar Nan Bashi

SERAP

kungiyar nan mai rajin tabbatar da adalci a hukumomi da ma’aikatun gwamnati SERAP, ke yin kira ga bankin duniya da ya dakatar da baiwa jihohin kasar nan 36 lamuni, saboda zargin karkatar da kudaden da suke yi

Bayanin hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da mataimakin daraktan kungiyar Kolawole  Oluwadare  ya fitar a ranar  lahadi.

Wasikar mai dauke da kwananann wata  25 ga watan da muke ciki, ta bukaci  bankin duniya  da  ya  gudanar da bincike  kan yadda  aka kashe kudin da  ya bayar  a matsayin bashi  da gwamnonin kasar nan suka karbo daga hannunsa,  sannan ya dena  bayar da bashin matukar  ya gano  akwai  lauje cikin nadi  a  bada  bashin.

Kungiyar  ta  ce  akwai bukatar  bankin duniyar  ya dena  baiwa  jihohi  bashi  har  sai sunyi cikakken bayani  na  gamsarwa kan yadda  suka kashe sauran basussukan da suka karba daga wajensa.