On Air Now

ZANGON BARKA DA SAFIYA

5:00am - 10:00am

Kungiyar 'Yan Jarida Ta Soki Matakin Da Hukumar NBC Ta Dauka Na Soke Lasisin Wasu Kafafen Yada Labarai 52

TAMBARIN KUNGIYAR 'YAN JARIDA

Kungiyar Yan Jarida ta kasa ta baiyana matakin da Hukumar Kula da kafafen Yada Labarai ta kasa NBC ta dauka na soke lasisin wasu kafafen yada labarai har 52 sakamakon taurin bashin da take binsu, a matsayin wani hukunci na gaggawa wanda zai maida hannun agogo baya.

Ta cikin wata sanarwa da shugaban kungiyar Chiris Isiguzo ya fitar, Yace hukumar ta dauki matakin ne batare da yin nazari da kuma tuntuba ba,  musamman la’akarin da halin rashin tsaro da kasa ke ciki.

Daga nan sai tayi kira ga hukumar NBC data  yi kaffa-kaffa kan matakin la’akarin  da yanayin tsaro da kasa ke ciki, tare da sake bada kofar  tattaunawa domin samar da masalaha akan matsalar.

A ranar juma’a ne Hukumar kula da Kafafen Yada Labarai ta kasa ta soke lasisin kafafen yada labarai  52 cikinsu hadda gidan Talabijin na  Silverbird da AIT da gidan Rediyon Raypower da sauransu skaamakon kin sabunta lasisinsu da suka kayi, wanda jimillar kudaden da take binsu zai kai naira bilyan 2 da milyan  66.